Gwamnatin ƙasar Uganda ta kama ‘yan Nijeriya 62 kan zargin gudanar da ayyukan ibada a wata coci ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamnatin ƙasar Uganda ta kama ‘yan Nijeriya 62 kan zargin gudanar da ayyukan ibada a wata coci ba bisa ƙa’ida ba.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar shige da fice ta ƙasar , ta ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da ta samu ne bayan ta gano cewa mutanen suna aiki a ƙasar ba tare da takardun izinin da ake buƙata ba.

Simon Peter Mundeyi, wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron cikin gidan ƙasar, ya ce sau da yawa ‘yan Nijeriya suna fitowa ne a matsayin masu wa’azin yaɗa bishara kuma suna aikata wasu ayyuka da suka saɓa wa doka.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana riƙe da su ne a wani wuri na ma’aikatar da ke Namanve, inda ake bincike a kansu wanda zai iya sa wa a tasa ƙeyarsu ko a ci tararsu ko kuma a hana su shiga ƙasar har abada.

Mundeyi ya ce bincike wucin-gadi ya nuna bayanai masu karo da juna daga bakin waɗanda ake zargin, yana mai ƙarawa da cewa wasu sun yi iƙirarin cewa da yaudara aka kai su Uganda da takardun ayyuka na bogi, yayin da ake zargin sauran da kasancewa masu damfara ta intanet da laifuka masu alaƙa da shi.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *