Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fara nazarin yiwuwar komawa wata jam’iyyar siyasa, bayan da tattaunawar da aka yi tsakaninsa da jam’iyyar APC ta kasa cimma matsaya.
Shugaban wani bangare na jam’iyyar PDP a jihar, karkashin jagorancin tsagin Tanimu Turaki, Samaila Adamu Burga, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Asabar.
Burga ya bayyana cewa duk da kokarin da shugabannin APC suka yi na jawo hankalin gwamnan, ba a samu amincewa kan wasu muhimman bukatu ba. Ya ce an fara tattaunawar ne ta hannun Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Yiltwada Netanwe, tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya kai ziyara Bauchi domin lallashin gwamnan.
Sai dai, ya ce tattaunawar ta tsaya cak ne sakamakon rashin jituwa kan tsarin rabon mukamai na kashi 60 da 40 da aka gabatar domin tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar.
A cewarsa, irin wannan tsari an taba amincewa da shi a wasu jihohi da gwamnoni suka koma APC, amma a wannan karon abin bai samu karbuwa ba.
Burga ya jaddada cewa ba zai yiwu wata gwamnati ta shigo jam’iyya tare da cikakken tsarinta daga matakin kasa zuwa jiha ba tare da samun isasshen iko a cikin jam’iyyar ba.
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed shi ne ke jagorantar wannan tattaunawa tun daga farko, amma daga bisani aka dakatar da ita bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki na PDP da kuma yin nazari mai zurfi.
Acewar Jaridar Aminiya a halin yanzu, Burga ya ce suna ci gaba da tuntubar wasu jam’iyyun siyasa domin ganin inda zai fi dacewa su koma, yana mai jaddada cewa kofarsu a bude take ga kowa domin tattaunawa — sai dai APC ba ta cikin zabin.
Ya kara da cewa PDP a Bauchi, tare da gwamnan da sauran shugabanni, na duba hanyoyin siyasa mafi dacewa da za su kare muradun al’ummar jihar.
Duk da cewa har yanzu ba a cimma matsaya kan sabuwar jam’iyya ba, ya ce za su zabi inda al’ummarsu za su samu damar tsayawa takara da kuma samun kwanciyar hankali a siyasance.
