Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai.

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai.

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, a shari’ar da ake tuhumarsa da almundahanar kuɗaɗe da kuma amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Darius Khobo, ya bayyana hukuncin ne bayan sauraron muhawarar ɓangarorin biyu, inda ya kuma dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa farkon watan Yunin 2026, tare da umarnin a riƙa gudanar da ita kullum.

Matakin kotun ya jawo tashin hankali a harabar kotun, inda wasu daga cikin magoya bayan El-Rufai suka fashe da kuka, suna nuna damuwa kan halin da ake ciki.

Lauyan wanda ake ƙara, Ubong Akpan (SAN), ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin, yana mai cewa kotun ta danganta ƙin bayar da belin da yiwuwar El-Rufai zai iya tsoma baki a bincike saboda kasancewarsa tsohon gwamna.

Sai dai ya jaddada cewa za su ƙalubalanci hukuncin ta hanyoyin shari’a, tare da zargin cewa shari’ar na da nasaba da siyasa, duk da cewa takardun tuhuma sun bayyana a matsayin na doka.

A halin yanzu, an shafe kusan kwanaki 62 El-Rufai yana tsare, tun bayan kama shi a watan Fabrairun 2026, baya ga ɗan lokacin da aka sake shi saboda rasuwar mahaifiyarsa.

Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda tara da suka haɗa da zargin karkatar da biliyoyin naira, karɓar kuɗin sallama fiye da ƙa’ida, da kuma ba da kwangiloli ba bisa doka ba.

Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *