Rundunar ‘yan sanda a Jihar Niger ta dakile wani yunƙurin fashi da makami a Minna, bayan da wasu matasa suka kai hari kan yankin Sauka zuwa Kahuta.

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Niger ta dakile wani yunƙurin fashi da makami a Minna, bayan da wasu matasa suka kai hari kan yankin Sauka zuwa Kahuta.

Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Tudun Wada, inda aka sanar da su cewa wasu matasa shida dauke da bindiga da makamai masu kaifi sun far wa mazauna yankin, suna kwace wayoyi da kuɗi.

Sai dai ɗaya daga cikin mazauna yankin ya yi jarumta, inda ya fafata da maharan har ya kwace adda daga hannun ɗaya cikinsu tare da raunata shi, lamarin da ya sa sauran suka tsere.

Jami’an tsaro sun ce sun tarar da wasu makamai da maharan suka bari a wurin, yayin da ake ci gaba da farautar su domin cafke su tare da kwato kayan da suka sace.

A wani lamari na daban kuma, ‘yan sanda sun kama wata mata mai suna Rukayya Muhammad a Kontagora bisa zargin safarar tabar wiwi, bayan da aka same ta da jaka cike da haramtacciyar ƙwayar.

Ta amsa cewa tana sayar da ita ga jama’a, kuma an riga an gurfanar da ita a kotu, yayin da bincike ke gudana domin gano sauran masu alaƙa da ita.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *