Wasu masana siyasa a Najeriya sun nuna shakku kan yawan ƙuri’un da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa Tinubu ya samu kusan ƙuri’u miliyan 11, inda ya kayar da abokin takararsa Stanley Osifo a zaɓen da aka gudanar a faɗin ƙasar.
Sai dai Farfesa Abubakar Kari na Jami’ar Abuja ya ce duk da cewa nasarar Tinubu ba abin mamaki ba ce, amma adadin ƙuri’un da aka sanar ya jawo tambayoyi daga mutane da dama.
A cewarsa, yadda aka ce an gudanar da zaɓe a dubban rumfunan ƙuri’a sannan aka samu irin wannan yawan ƙuri’u na iya sa jama’a su yi shakku kan sahihancin sakamakon.
Jihohin da Tinubu ya fi samun ƙuri’u sun haɗa da Legas, Adamawa, Kaduna, Imo da Kano.
APC ta ce zaɓen ya gudana ne a ƙananan hukumomi 774 na Najeriya, sannan ta miƙa wa Tinubu shaidar lashe zaɓen a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2027.
