An gano gawar wata budurwa mai shekaru 29 a cikin wani tafki a garin Abuja.

An gano gawar wata budurwa mai shekaru 29 a cikin wani tafki a garin Abuja.

Mamaciyar mai suna Blessing Moshood ta kasance wadda ta kammala karatu a Jami’ar Jihar Kogi, inda ta samu digiri mai daraja ta biyu a fannin Sociology.

Rahotanni sun nuna cewa Blessing ta bar gida ne da daddare bayan wata tattaunawa ta waya, sannan daga baya ta sanar da iyalanta cewa za ta dawo domin daukar cajar wayarta. Sai dai daga wannan lokaci ba a sake jin ta ba.

Washegari ne iyalan suka shiga firgici bayan samun bayanin cewa an gano gawar wata mata a cikin tafki. Bayan bayanin siffofi da kitson gawar, iyalan suka fahimci cewa Blessing ce.

A cewar iyalanta, jami’an ’yan sanda sun sanar da su cewa an tsinci gawar marigayiyar a tube, sannan aka kai ta dakin ajiye gawa da ke Mararraba a Jihar Nasarawa.

Makwabta da abokan arziki sun bayyana marigayiyar a matsayin mace mai nutsuwa, son jama’a da kuma hazaka a bangaren karatu.

Wasu mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike tare da daukar matakan dakile ayyukan bata-gari da ke haddasa rashin tsaro a yankin.

Rundunar ’yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *