Ba za a iya samar da ingantaccen tsaro a Najeriya da ƙarfi  ba — IG Disu.

Ba za a iya samar da ingantaccen tsaro a Najeriya da ƙarfi ba — IG Disu.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa amfani da ƙarfin jami’an tsaro kaɗai ba zai wadatar wajen tabbatar da zaman lafiya ba, sai an samu haɗin kai da amincewar al’umma.

Disu ya bayyana hakan ne a wajen bikin rufe wani taron horas da jami’an hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda, wanda aka gudanar a birnin Legas.

Mataimakin Babban Sufeton ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar Rundunar, DIG Simeon Akpanidum, ne ya wakilce shi a taron.

A cikin jawabin da aka gabatar a madadinsa, IGP Disu ya ce kyakkyawar alaƙa tsakanin jami’an tsaro da al’umma ita ce ginshiƙin samar da tsaro mai ɗorewa a ƙasar.

Ya bayyana cewa ƙalubalen tsaro na wannan zamani na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, kafafen yaɗa labarai, ƙwararru da kuma ‘yan ƙasa domin samun mafita mai ɗorewa.

Babban Sufeton ya kuma jaddada muhimmancin gina amincewar jama’a ga hukumomin tsaro ta hanyar gudanar da aiki cikin gaskiya da riƙon amana, tare da ƙarfafa shigar matasa cikin shirye-shiryen tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *