Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da wani yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon bayan sabbin hare-haren da aka kai cikin dare, waɗanda suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 47, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana.
Mahukuntan Isra’ila sun ce hare-haren da suka kai martani ne ga ayyukan Hezbollah, ciki har da wani hari da aka kai cikin dare wanda ya yi ajalin sojojin Isra’ila huɗu.
An fara aiwatar da tsagaita wutar ne da ƙarfe 4:00 na yamma agogon ƙasar, sai dai rahotanni daga yankin sun nuna cewa an ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe da hare-hare a wasu wurare duk da yarjejeniyar.
Masu sa ido na ganin wannan tsagaita wutar wata muhimmiyar gwaji ce ga yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimma a farkon wannan makon, wadda ta tanadi dakatar da ayyukan soji a yankunan rikici da suka haɗa da Lebanon.
Sai dai Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta bayyana cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakin gaggawa kan duk wata barazana da za ta iya tasowa, tare da mayar da martani kan duk wani hari ko matakin da Hezbollah za ta ɗauka.
A nasa ɓangaren, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi gargaɗin cewa idan Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar, Amurka ce za ta ɗauki alhakin abin da zai biyo baya.
Yarjejeniyar na zuwa ne a wani lokaci da ake ƙoƙarin rage tashin hankalin da ya daɗe yana addabar yankin Gabas ta Tsakiya, inda kasashen duniya ke sa ido kan yadda bangarorin za su mutunta sharuddan da suka amince da su.
