Tsagin ’yan adawa a Majalisar Wakilai ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage mayar da hankali kan siyasar zaɓen 2027, tare da ba da fifiko wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar Najeriya.
Da yake jawabi a Abuja, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Fred Agbedi, ya bayyana damuwa kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga, garkuwa da mutane, talauci da tsadar rayuwa. Ya ce hare-haren da suka haɗa da sace ɗalibai da kashe-kashe sun nuna cewa matsalar tsaro na ci gaba da ta’azzara.
’Yan adawar sun buƙaci shugaban ƙasar ya aiwatar da wani shiri na gaggawa domin inganta tsaro, ceto waɗanda aka sace da kuma sake fasalin tsarin tsaron ƙasa. Sun kuma nuna damuwa kan matakin soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa, suna mai kira ga INEC da kotuna su kare tsarin dimokuraɗiyya.
A wani ɓangaren kuma, tsohon gwamnan mulkin soja na Kaduna, Abubakar Dangiwa Umar, ya buƙaci Tinubu ya bai wa kare rayuka da dukiyoyin jama’a muhimmanci, yana mai cewa babu ci gaba mai ɗorewa idan babu tsaro.
Rahoton Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC) ya nuna cewa an kashe mutane 390 tare da sace wasu 202 a watan Mayun 2026.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakan yaƙi da rashin tsaro. Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a ɗauki sabbin ’yan sanda sama da 50,000, tare da ƙara tallafa wa ɓangaren tsaro domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
