Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta sanar da kai wasu hare-hare kan wuraren sojojin Isra’ila da ke kudancin ƙasar, a wani sabon salo na rikicin da ke ci gaba da ƙamari a yankin.
A cikin wata sanarwa, Hezbollah ta ce mayaƙanta sun kai hari kan hedkwatar rundunar sojin Isra’ila da ke Naqoura ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa nau’in Ababil, inda ta yi iƙirarin kai hari kai tsaye kan wurin.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta kai wani hari kan sojojin Isra’ila da ke yankin Hadada ta amfani da jirage marasa matuƙa guda biyu, tare da harba rokoki da harsasan manyan bindigogi zuwa wuraren da ke kusa da sansanin Beaufort Castle.
A nata ɓangaren, rundunar sojin Isra’ila ta ce cikin sa’o’i 48 da suka gabata ta kai hare-hare sama da 150 a yankunan kudancin Lebanon, inda ta bayyana cewa hare-haren sun nufi wurare da kayayyakin da take zargin suna da alaƙa da Hezbollah.
Rikicin ya ƙara ɗaukar sabon salo bayan da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) suka yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan wata motar sojojin Lebanon a yankin Nabatieh.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin mutuwar sojojin Lebanon uku, lamarin da ya ƙara tayar da hankali kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a kan iyakar Lebanon da Isra’ila.
Ana ci gaba da fargabar cewa ƙaruwar hare-hare tsakanin bangarorin biyu na iya jefa yankin cikin wani sabon yanayi na tashin hankali mai muni.

