A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa ranar Laraba, Fubara ya bayyana cewa bayan doguwar tattaunawa da iyalansa, abokai da kuma abokan siyasarsa, ya yanke shawarar janyewa daga takarar domin bai wa zaman lafiya da hadin kan jihar fifiko.
Fubara ya ce duk da cewa yanke wannan shawara ba abu ne mai sauki ba, yana da cikakken niyyar mara wa duk wanda ya lashe tikitin jam’iyyar baya a zaben 2027. Ya bayyana cewa shugabanci yana bukatar sadaukarwa, kuma wani lokaci buri na kai dole ne ya kauce domin amfanin jama’a gaba daya. Ya kara da cewa Jihar Rivers ta fi kowane mutum muhimmanci, musamman a wannan lokaci da jihar ke bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnan ya kuma gode wa magoya bayansa bisa addu’o’i, biyayya da sadaukarwar da suka nuna a lokacin tafiyar siyasar. Ya amince cewa wasu daga cikin magoya bayansa za su ji takaici saboda matakin da ya dauka, amma ya bayyana cewa shirunsa a ‘yan makonnin baya na da manufa ta musamman domin kare muradun jihar. Hakan na zuwa ne bayan wani jigo na APC a Rivers, Tonye Cole, shi ma ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamna saboda hadin kan jam’iyyar.

