Rahotanni sun ce wasu matasa biyu masu ɗauke da makamai sun kutsa cikin Cibiyar Musulunci ta San Diego inda suka bude wuta a ranar Litinin, lamarin da ya jawo mutuwar jami’in tsaro da wasu mutum biyu da ke cikin masallacin.
Shugaban cibiyar kuma limamin masallacin, Taha Hassane, ya bayyana harin a matsayin abin tashin hankali, yana mai cewa ba su taɓa ganin irin wannan mummunan al’amari a wurin ibadar ba.
Jami’an tsaro da suka isa wurin sun gano gawarwakin mutane uku da aka kashe, yayin da suka yabawa jami’in tsaron da ya mutu bisa kokarin da ake ganin ya taimaka wajen dakile karin asarar rayuka.
Bayan harin, ’yan sanda sun gano gawarwakin wadanda ake zargi da kai harin — matasa masu shekaru 17 da 18 — a cikin wata mota, inda ake zargin sun kashe kansu bayan aikata harin.
Kwamishinan ’yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya ce ana gudanar da bincike tare da hadin gwiwar Hukumar FBI domin gano ko harin yana da nasaba da kiyayya addini.
Hukumomi sun tabbatar da cewa dukkan daliban makarantar rana da ke cikin harabar masallacin suna cikin koshin lafiya bayan aukuwar lamarin.
Bincike ya nuna cewa mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargi ta sanar da ’yan sanda tun kafin harin, bayan ɗanta ya gudu daga gida dauke da bindigogi uku da kuma motarta.
Ta kuma bayyana cewa matashin yana tare da wani abokinsa, kuma dukkansu sun sanya kayan sojoji kafin daga bisani a samu rahoton harin da aka kai masallacin.
Hukumar FBI ta bayyana sunayen wadanda ake zargi da Caleb Liam Vazquez mai shekara 18 da Cain Lee Clark mai shekara 17, wadanda dukkansu mazauna San Diego ne.
Jami’an bincike sun ce ana zargin matasan sun fara haduwa ne ta intanet kafin daga baya suka shirya kai harin tare.

