Kimanin jihohi 21 a Najeriya, ciki har da Rivers da Kano, har yanzu ba su fara aiwatar da cikakken ikon tafiyar da harkokin wutar lantarki a jihohinsu ba.

Kimanin jihohi 21 a Najeriya, ciki har da Rivers da Kano, har yanzu ba su fara aiwatar da cikakken ikon tafiyar da harkokin wutar lantarki a jihohinsu ba.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa jihohi 15 sun riga sun shiga tsarin kasuwar samar da wutar lantarki mai zaman kanta, inda suka fara ɗaukar matakan da suka dace wajen tafiyar da harkokin a yankunansu.

Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa ta bayyana cewa jihohin da suka kammala shirye-shiryensu su ne ke da alhakin bunƙasa kasuwar wutar lantarki, jawo masu zuba jari, tsara haraji, da kuma kare haƙƙin masu amfani da wutar lantarki a yankunansu.

A cewar hukumar, sauye-sauyen na da alaƙa da dokar wutar lantarki ta 2023, wadda ta bai wa jihohi ikon samarwa da rarraba wutar lantarki, tare da kafa dokoki da tsarin gudanarwa a matakin jiha.

Daga cikin jihohin da suka riga suka fara aiwatar da tsarin akwai Enugu, Ekiti, Ondo, Imo, Oyo, Edo, Kogi, Legas, Ogun, Neja, Filato, Abia, Nasarawa, Anambra da kuma Bayelsa.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *