Wani saɓani kan kuɗi Naira 200 ya rikide zuwa fadan da ya yi sanadin mutuwar wani magini  a Jhar Ogun.

Wani saɓani kan kuɗi Naira 200 ya rikide zuwa fadan da ya yi sanadin mutuwar wani magini a Jhar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, Isreal Ayomide, ya rasa ransa ne bayan wani da ake zargi mai suna Aboy ya daba masa wuƙa a wata masana’antar bulo da ke yankin Ota.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Afrilu a yankin Ori-Ade, inda rikicin da bai ɗauki lokaci ba ya koma rikicin da ya kawo ƙarshen rayuwa. Shaidu sun ce cikin ’yan mintoci kaɗan ne faɗar ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka kai wa Ayomide hari.

An yi ƙoƙarin kai shi asibiti cikin gaggawa, amma ya riga mu gidan gaskiya kafin a samu taimako.

Bayan faruwar lamarin, wanda ake zargin ya tsere daga wurin, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Jaridar aminiya ta rawaito cewa mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda aka tafiyar da lamarin, inda suka zargi jami’an tsaro da rashin gaggauta neman wanda ake zargin, tare da cewa an tsare wasu da suka kai rahoto maimakon a bi sawun wanda ya aikata laifin.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *