Yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, masana harkokin siyasa sun yi gargaɗin cewa zarge-zargen da ake yi wa shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, na iya tasiri ga amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Binciken Jaridar Aminiya ya nuna a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, an yi ta muhawara kan zargin cewa shugaban hukumar na da alaƙa da jam’iyyar APC mai mulki, bayan bayyanar wani shafi a kafafen sada zumunta da ake danganta shi da goyon baya ga jam’iyyar. Sai dai hukumar INEC ta musanta zargin, tana mai cewa shugaban nata ba shi da irin wannan shafi, kuma ana ƙoƙarin ɓata masa suna ne.
Haka kuma, wasu ƙungiyoyi da malaman addini sun zargi Amupitan da nuna ɓangaranci na addini, lamarin da ya janyo kiraye-kirayen a sauke shi daga muƙaminsa.
Jam’iyyun adawa, ciki har da ADC da PDP, sun nuna rashin amincewa da shugabancinsa, inda wasu daga cikinsu suka gudanar da zanga-zanga tare da neman a sauke shi ko a cire shi daga mukaminsa. Sun bayyana fargabar cewa zaɓen 2027 ba zai kasance mai cike da adalci ba idan har ya ci gaba da jagorantar hukumar.
Masana sun bayyana cewa ko da ba a tabbatar da gaskiyar zarge-zargen ba, tasirinsu a zukatan jama’a ya riga ya bayyana, wanda hakan ka iya haifar da ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a ko kuma rikice-rikice bayan sanar da sakamakon zaɓe.
Sai dai INEC ta buƙaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa ta ɗauki matakin shari’a kan masu yaɗa irin waɗannan bayanai.
Masana sun jaddada cewa tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaɓe shi ne mafi muhimmanci domin kare dimokraɗiyyar ƙasa da kuma kauce wa duk wani rikici bayan zaɓe.

