Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya bayyana cewa wannan yarjejeniya na da matuƙar muhimmanci wajen rage tashin hankali da kuma taimakawa wajen kawo ƙarshen faɗace-faɗacen da suka daɗe suna addabar yankin.
Sai dai yarjejeniyar ta fuskanci suka mai tsanani daga wasu manyan jami’an gwamnatin Isra’ila, waɗanda suka nuna rashin amincewarsu da yadda aka gudanar da tattaunawar.
Isra’ila ta bayyana cewa ba a nemi ra’ayinta ko tuntubarta ba kafin Amurka da Iran su kai ga cimma wannan yarjejeniya, duk da kasancewarta muhimmin ɓangare a rikicin yankin.
Ministan Kuɗi na Isra’ila ya soki matakin, yana mai cewa yarjejeniyar na iya haifar da illa ga tsaron Isra’ila da kuma zaman lafiyar duniya baki ɗaya.
Haka kuma, Ministan Tsaron Isra’ila ya jaddada cewa sojojin ƙasarsa ba za su fice daga yankunan kudancin Lebanon da suka mamaye ba, duk da ƙoƙarin da ake yi na samar da tsagaita wuta ta hanyar wannan yarjejeniya.
Lamarin na ci gaba da jan hankali a matakin ƙasa da ƙasa, yayin da ake sa ido kan yadda yarjejeniyar za ta shafi makomar rikicin da kuma zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
