Kotu ta ba Hukumar INEC Umarnin Soke Rajistar Jam’iyyar ADC da Wasu Jam’iyyu daban.

Kotu ta ba Hukumar INEC Umarnin Soke Rajistar Jam’iyyar ADC da Wasu Jam’iyyu daban.

 

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta cire rajistar jam’iyyar ADC tare da wasu jam’iyyu hudu, bayan kotun ta gano cewa ba su cika wasu muhimman sharuɗɗan da doka ta gindaya wa jam’iyyun siyasa ba.

Hukuncin wanda Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke, ya bayyana cewa jam’iyyun sun kasa samun kaso 25 cikin 100 na ƙuri’un da ake buƙata a zaɓukan da suka gabata, lamarin da kotun ta ce ya sa suka gaza cika sharuddan ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa masu rijista.

Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da African Democratic Congress (ADC), Accord (A), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) da kuma Zenith Labour Party (ZLP).

Baya ga umarnin soke rajistar, kotun ta kuma hana jam’iyyun damar shiga duk wasu zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen shekarar 2027, har sai sun cika dukkan ka’idojin da doka ta tanada.

Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da Ƙungiyar Tsofaffin ’Yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta shigar, inda ta zargi jam’iyyun da rashin cika sharuɗɗan da suka shafi samun goyon bayan jama’a da kuma sakamakon zaɓe.

Kafin yanke hukunci, kotun ta yi watsi da wasu ƙorafe-ƙorafen farko da waɗanda ake ƙara suka gabatar, sannan daga bisani ta tabbatar da hukuncin da ya shafi makomar jam’iyyun.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *