’Yan Najeriya Sun Nemi Mafaka a Ofishin Jakadanci a Afirka ta Kudu Saboda Fargabar Hare-Hare

’Yan Najeriya Sun Nemi Mafaka a Ofishin Jakadanci a Afirka ta Kudu Saboda Fargabar Hare-Hare

domin neman mafaka sakamakon fargabar hare-haren kyamar baki da suka addabi wasu yankuna.

Rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu sun shiga cikin damuwa da rashin tabbas duk da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka na kwashe ’yan ƙasar da ke zaune a Afirka ta Kudu zuwa gida Najeriya.

A wasu bidiyoyi da suka karade kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai, an hangi taron ’yan Najeriya suna cunkushe a harabar Ofishin Jakadancin Najeriya, suna jiran karin bayani kan shirin jigilar su zuwa ƙasar.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa mutanen da suka yi rajista ko kuma suka tuntubi ofishin jakadancin ne kawai aka tsara za a fara kwashewa a jirgin da aka shirya ya tashi a daren Litinin, lamarin da ya jefa wasu da ba su shiga cikin jerin sunayen ba cikin rashin tabbas.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa an bai wa mata da yara ƙanana fifiko a cikin shirin fitar da mutanen daga ƙasar, inda aka tanadar musu wuraren zama a harabar ofishin jakadancin yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen kwashe sauran ’yan Najeriya da suka rage.

Jami’an ofishin jakadancin na ci gaba da tsara hanyoyin da za a bi domin tabbatar da cewa an fitar da sauran mutanen cikin tsari da aminci, yayin da ake ci gaba da sa ido kan halin tsaro a wasu sassan Afirka ta Kudu.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *