Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda Biyu, Sun Kama Mutane Takwas a Kaduna da Zamfara

Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda Biyu, Sun Kama Mutane Takwas a Kaduna da Zamfara

Rundunar haɗin gwiwar sojoji da ke gudanar da aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma ta sanar da kashe wasu ’yan ta’adda biyu tare da kama mutane takwas da ake zargi da hannu wajen ayyukan ta’addanci a jihohin Kaduna da Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gudanar da samamen ne a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na murƙushe ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankin.

A cewarsa, yayin wani sintiri da dakarun soji tare da jami’an sa-kai suka gudanar a ƙananan hukumomin Giwa da Kaduna ta Arewa, sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda da ke tafiya da mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji ta hanyar amfani da babura.

Ya ce an yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya sa maharan suka rika watsar da baburansu tare da tserewa domin ceton rayukansu.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun samu nasarar ceto mutum guda daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su. Sai dai an tabbatar da mutuwar wani mutum bayan maharan sun harbe shi kafin isowar jami’an tsaro.

A wani samame daban, sojoji sun kai ɗauki ƙauyen Dariya da ke Ƙaramar Hukumar Giwa bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari yankin, inda suka kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu uku. Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun fatattaki maharan bayan isa wurin.

Haka kuma a Jihar Zamfara, jami’an tsaro sun kama wasu mutum biyu a ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Gusau bisa zargin taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda.

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kama na da alaƙa da samar da magunguna da wasu kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda da ke aiki a yankin.

Rundunar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kai farmaki kan maboyar masu aikata laifuka tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da al’umma domin inganta tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *