Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu lokacin da tsohon jami’in sojan da matarsa ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina.
Majiyoyi sun ce maharan sun tare motar da ma’auratan ke ciki kafin su yi awon gaba da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.
Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga yayin harin, sai dai ya samu damar tserewa daga hannun maharan.
Ya zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina da Rundunar Sojin Najeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da sace tsohon jami’in sojan da matarsa ba.
Ana sa ran hukumomin tsaro za su yi karin bayani kan lamarin yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda aka kai wadanda aka sace da kuma ceto su.
