Ana ci gaba da muhawara a Jihar Kano kan kwatanta aikin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, da wanda ya gabace shi, Muhammad Garba, yayin da ake nazarin tasirin da kowannensu ya yi a ma’aikatar.
Masu bibiyar harkokin siyasa na ganin cewa muhawarar ba ta tsaya kan neman mulki kawai ba, illa ta shafi hangen nesa, ƙwarewa da irin nasarorin da aka samu a lokacin jagorancinsu.
Muhammad Garba ya shafe shekaru takwas yana jagorantar ma’aikatar, yayin da Ibrahim Waiya ya yi kusan shekara ɗaya da rabi kacal a kan mukamin. Sai dai magoya bayan Waiya na cewa cikin ɗan gajeren lokacin da ya yi, ya kawo sabbin dabarun sadarwa da kuma inganta yaɗa ayyukan gwamnati ga jama’a.
A gefe guda kuma, masu goyon bayan Garba na bayyana gogewarsa da tsawon lokacin da ya yi a ma’aikatar a matsayin muhimman abubuwan da suka bambanta shi.
Duk da nasarorin da ake dangantawa da Waiya, akwai masu kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sake duba shugabancin ma’aikatar, yayin da wasu ke zargin ana ƙoƙarin ɓata sunansa saboda wasu muradun siyasa.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce abin da ke faruwa a Kano a yanzu tamkar gwagwarmaya ce tsakanin gogewa da kuma sabbin dabaru. Sun yi imanin cewa ya kamata a bai wa jama’a damar jin ra’ayoyin bangarorin biyu domin tantance wanda ya fi dacewa wajen taimaka wa gwamnati ta isar da manufofinta ga al’umma.
Yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, masu lura da al’amuran siyasa na ganin irin wannan muhawara za ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar siyasar Kano da kuma tantance waɗanda za su jagoranci yaɗa manufofin gwamnatin jihar.
