Cutar kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Jihar Borno, inda ta yi sanadin mutuwar mutum 108 tare da kamuwa da sama da mutum 13,000 tun bayan ɓullar ta a farkon watan Mayun 2026.
Bayanan da Ma’aikatar Lafiya da Kula da Lafiyar Jama’a ta jihar ta fitar sun nuna cewa zuwa ranar 18 ga watan Yuni, adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 13,234 a sassa daban-daban na jihar.
Rahoton ya bayyana cewa daga cikin mutanen da suka rasu, 71 sun mutu ne a cibiyoyin lafiya yayin da wasu 37 suka rasa rayukansu a cikin al’umma kafin su samu kulawar likitoci.
Haka kuma, annobar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 17 daga cikin 27 da ke jihar, lamarin da ke nuna yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa cikin sauri.
Birnin Maiduguri ne ya fi fuskantar matsalar, inda aka samu mutum 7,083 da suka kamu da cutar, sai Jere mai mutum 3,403. Haka nan ƙananan hukumomin Konduga da Monguno na daga cikin yankunan da annobar ta fi shafa.
A ranar 18 ga watan Yuni kaɗai, an yi rajistar sabbin masu kamuwa da cutar 236, yayin da mutum 226 ke karɓar magani a cibiyoyin lafiya daban-daban a faɗin jihar.

