Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da babbar damar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 — Hon Oseni

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da babbar damar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 — Hon Oseni

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ido/Ibarapa a Jihar Oyo, Honorabul Aderemi Oseni, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da babbar damar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, bisa abin da ya bayyana a matsayin nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.

Oseni, wanda ke neman tikitin Sanatan Oyo ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya ce ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun ƙara masa karɓuwa a tsakanin al’umma, yana mai cewa jam’iyyun adawa za su fuskanci ƙalubale wajen hana shugaban ƙasar samun wa’adi na biyu.

Ya bayyana wannan ra’ayi ne yayin wani shirin tallafa wa manoma da ya gudanar a Ibadan ranar Litinin, inda dubban mutane suka amfana da kayan aikin noma, takin zamani, sinadarai da sauran kayan tallafin noma.

Dan majalisar, wanda kuma ke shugabantar Kwamitin Kula da Hukumar Gyaran Hanyoyin Tarayya a Majalisar Wakilai, ya ce zai ci gaba da wayar da kan jama’a da kuma tara goyon baya ga Shugaba Tinubu ta hanyar ƙungiyar Remi Oseni Committee of Friends.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta taimakawa wajen samar wa shugaban ƙasar kuri’u masu yawa daga Jihar Oyo a zaɓen 2027, yana mai cewa yana da yakinin cewa al’ummar jihar za su mara masa baya.

A cewarsa, shekara huɗu kacal ba za su wadatar wajen magance tarin matsalolin da ƙasar ta gada daga baya ba, don haka akwai buƙatar a bai wa Tinubu damar ci gaba da shirye-shiryensa ta hanyar sake zaɓensa domin wa’adi na biyu.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *