Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta sanya ranar 22 ga watan Yuli, 2026 domin karɓar jawabai na ƙarshe daga ɓangarorin da ke ƙarar da ke neman soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Kudu.
Shari’ar dai ta samo asali ne daga ƙarar da Hon. Bilyaminu Babadidi ya shigar, inda yake ƙalubalantar sahihancin ayyana Jerry Joseph Damara a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen sanatan yankin.
A zaman kotun da Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ke jagoranta, ɓangaren mai ƙara ya gabatar da shaidu huɗu tare da miƙa wasu takardu domin tabbatar da ikirarinsu.
Shaidun sun yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani yadda ya kamata ba a rumfunan zaɓe da ƙananan hukumomin da ke mazabar, tare da cewa ba a tura jami’ai ko kayan aikin zaɓe zuwa wuraren da ya kamata ba.
Sun kuma shaida wa kotu cewa mai ƙarar ya kai koken lamarin ga Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na jam’iyyar APC, amma ba a samu wani mataki daga jam’iyyar ba.
A nasa ɓangaren, APC ta gabatar da shaida guda ɗaya, Rabilu Musa, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kwamitin da ya kula da zaɓen fidda gwani daga hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.
Shaidan ya tabbatar wa kotu cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani a ranar 18 ga watan Mayun 2026, kuma ya haɗa da zaɓen ɗan takarar Sanatan Gombe ta Kudu.
Sai dai yayin amsa tambayoyin lauyoyi, ya amince cewa ba a gabatar da kundin sunayen masu kaɗa ƙuri’a a gaban kotu a matsayin hujja ba.
Bayan kammala sauraron shaidu da karɓar hujjoji daga kowane ɓangare, kotun ta ayyana cewa an rufe matakin gabatar da shaidu, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Yuli domin sauraron jawabai na ƙarshe kafin yanke hukunci kan lamarin.

