Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya Bukaci Gwamna Abba Ya Ɗauki Tsauraran Mataki Kan Masu Nuna Masa Rashin Girmamawa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya Bukaci Gwamna Abba Ya Ɗauki Tsauraran Mataki Kan Masu Nuna Masa Rashin Girmamawa.

 

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya nuna cikakken iko da ƙarfin gwamnati wajen fuskantar duk masu ƙoƙarin raina shugabanci ko tayar da tarzoma a siyasance.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ziyarar Hawan Nassarawa da ya kai wa gwamnan domin taya shi murnar Babbar Sallah tare da ƙarfafa alaƙar masarauta da gwamnati.

A cikin jawabin nasa, Sanusi II ya ce zaman lafiya da adalci ba sa tabbata sai gwamnati ta nuna ƙarfi a lokacin da ya dace. Ya yabawa gwamnatin Abba saboda ayyukan ci gaba da take yi musamman a fannoni kamar ilimi, lafiya da tallafa wa al’umma.

Sai dai Sarkin ya nuna damuwa kan yadda wasu ke amfani da haƙurin gwamnati wajen aikata abubuwan da suka saɓa wa doka, yana mai cewa mutumin da bai cancanci girmamawa ba idan aka yi masa sassauci zai iya ɗaukar hakan a matsayin rauni.

Ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Kano za ta fito fili ta tabbatar wa kowa cewa akwai cikakkiyar gwamnati mai iko a jihar, yana mai jaddada cewa duk wanda ya bi doka zai zauna lafiya, wanda kuma ya ƙi bin doka ya fuskanci hukunci.

Sanusi II ya kuma bayyana cewa shi da masarautarsa a shirye suke su mara wa gwamnatin baya a duk wani mataki da za ta ɗauka domin kare mutuncin Kano da tabbatar da zaman lafiya.

A nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Sarkin Kano bisa shawarwari da goyon bayan da yake ba gwamnatin jihar. Ya bayyana cewa rashin gudanar da Hawan Daushe kamar yadda aka saba ya samo asali ne daga matsalolin tsaro da kuma ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnan ya ce shirun da yake yi ba tsoro ba ne, illa hikima da ƙoƙarin kauce wa tashin hankali wanda zai iya jawo asarar rayuka musamman ga mata, yara da sauran jama’ar da suka fito domin bukukuwan sallah.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa ba ya jin tsoron wani mahaluki face Allah, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare jihar daga rikice-rikice da rashin tsaro.

An dai dade ana fuskantar ce-ce-ku-ce kan batun masarautar Kano, lamarin da ya sa jami’an tsaro ke dakatar da wasu hawan sallah saboda fargabar tashin hankali tsakanin bangarorin masu biyayya ga Sarki Muhammadu Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *