Rukunin farko na maniyyatan Jihar Kano sun isa birnin Madina na ƙasar Saudiyya domin fara gudanar da ibadar Hajjin shekarar 2026.

Rukunin farko na maniyyatan Jihar Kano sun isa birnin Madina na ƙasar Saudiyya domin fara gudanar da ibadar Hajjin shekarar 2026.

Maniyyatan sun sauka lafiya a safiyar Asabar da misalin ƙarfe 7:35 agogon Najeriya, bayan tashinsu daga Kano da tsakar dare cikin jirgin kamfanin Max Air.

Jimillar alhazan da suka yi tafiyar farko sun kai 558, ciki har da maza 333 da mata 225.

Mahukunta sun bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Dala da Fagge da Gwale da Ungoggo.

Saukar tasu na daga cikin shirye-shiryen da ake yi domin gudanar da aikin Hajji cikin tsari da nasara a bana.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *