
Hukumar Tace Fina-finai da daba’i ta Jihar Kano ta dakatar da jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan, daga gudanar da harkokin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.
wannan na cikin sanarwar da jamiʼin yaɗa labaran hukumar Comrade Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha.
Sanarwar ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan bayyanar jaruman biyu a wani bidiyo da ta bayyana a matsayin wanda ya saɓa da tarbiyya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa dokar hukumar ta ba ta damar dakatar da duk wani ɗan masana’antar Kannywood daga gudanar da harkokin fim a Kano, tare da gargadin cewa karya dokar na iya jawo hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.
Shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha, ya ja hankalin ’yan masana’antar Kannywood da su guji duk wani abu da ka iya zubar musu da mutunci ko taɓa ƙimar masana’antarsu.
