Rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC ya sake ɗaukar sabon salo bayan kotu ta dakatar da sauraron ƙara.

Rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC ya sake ɗaukar sabon salo bayan kotu ta dakatar da sauraron ƙara.

An shiga wani sabon yanayi na rashin tabbas a jam’iyyar ADC bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da sauraron shari’ar da ake yi kan shugabancin jam’iyyar.

Shari’ar dai ta samo asali ne daga ƙarar da Nafi’u Bala Gombe ya shigar, inda yake ƙalubalantar shugabancin Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar ADC.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya sanar da dakatar da zaman kotun ba tare da sanya sabuwar rana ba, bayan mai ƙarar ya bayyana cewa ya nemi a sauya alƙalin da ke sauraron shari’ar zuwa wani daban.

Matakin ya jawo martani daga jam’iyyar ADC, wadda ta nuna damuwa kan yadda lamarin zai iya kawo cikas ga shirye-shiryenta na siyasa kafin babban zaɓe mai zuwa.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa dakatar da shari’ar na iya jefa jam’iyyar cikin yanayin ruɗani da rashin tabbas.

A cewarsa, akwai alamun cewa ana ƙoƙarin sauya alkiblar shari’ar ta hanyar cire ta daga hannun mai shari’ar da ke kula da ita a yanzu.
Shi ma wani lauya mai zaman kansa a Kano, Barista Haruna Zakari, ya bayyana cewa jinkirin sauraron shari’ar ka iya zama barazana ga ADC, musamman ganin cewa jam’iyyar na son a warware rikicin cikin gaggawa kafin wa’adin hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC.

Ya ƙara da cewa mafi dacewa a yanzu shi ne jam’iyyar ta nemi shugaban alkalan Babbar Kotun Tarayya ya shiga tsakani domin tabbatar da an ci gaba da sauraron ƙarar cikin sauri.

Tun farko dai Kotun Ƙoli ta tabbatar da shugabancin ɓangaren Sanata David Mark, sannan ta mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Tarayya domin a ci gaba da sauraron ƙorafe-ƙorafen da aka shigar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *