A cikin wata sanarwa da shugaban ofishin kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Volker Turk ya fitar a yau, ya ce tun bayan ƙaddamar da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka yi a Iran a ƙarshen watan Fabrairu, an zartarwa aƙalla mutane 9 hukuncin kisa sakamakon zanga-zangar da ta barke a ƙasar a watan Janairun, sannan akwai wasu mutum 10 da aka zarga da kasance wa mambobin a ƙungiyoyin ƴan adawa sai kuma wasu mutum biyu da aka kashe bisa zargin leken asiri.
Ofishin ya ƙara da cewa sama da mutane dubu 4 ne aka yi ƙiyasin an kama su a Iran ɗin, bisa dalilan da suka shafi tsaron ƙasar.
Rahoton ya kuma ce akwai da dama daga cikin fursunonin da ake tsare da su a ƙasar da aka nema aka rasa, ya yin da wasu ke fuskantar azabtarwa da wulakanci da kuma kisan gilla.
Don haka ne Volker Turk, ya buƙaci hukumomin Iran da su dakatar da zartar da hukuncin kisa, tare da maye hakan da wani hukunci na daban, da kuma yin adalci a yayin sauraron shari’un waɗanda ake zargi.
