Wannan ne lokaci mafi tsawo da jirgin – wanda ke ɗaukar jiragen yaƙi, kuma suke sauka a kansa – ya yi tun bayan yaƙin Vietnam.
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegsett ya je tashar ruwa ta Norfolk da ke jihar Virginia domin tarbar jirgin, wanda shi ne mafi girma da ke jiragen sama.
A cewar sojojin Amurka, jirgin ta taimaka a hare-haren da ƙasar ta ƙaddamar a yankin Karebiyan, inda sojojin Amurka suka ƙaddamar da hare-hare kan ƙananan jiragen ruwan masu safarar ƙwaya, tare da ƙwace tankokin mai da kuma kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro da mai ɗakinsa.
Daga nan kuma jirgin ya nufi yankin Gabas ta Tsakiya, domin taimakawa a hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kan Iran.
A tsawon wannan lokaci, akwai lokacin da gobara ta tashi a sashen wanke-wanke na jirgin inda ta ji wa ma’aikata biyu mummunan raunuka tare da lalata kusan gadaje 100.
An kuma riƙa samun rahotonnin matsaloli a sashen banɗakunan jirgin da sashen tsaftace shi.

