Kwamitin da gwamnatin Iran ta kafa domin tsara harkokin sadarwar intanet ya gudanar da zama na huɗu ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa na farko, Mohammad Reza Aref.

Kwamitin da gwamnatin Iran ta kafa domin tsara harkokin sadarwar intanet ya gudanar da zama na huɗu ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa na farko, Mohammad Reza Aref.

A yayin taron, an cimma matsaya kan wasu muhimman shawarwari da suka shafi dawo da ayyukan intanet, kuma za a miƙa su ga ma’aikatar sadarwa domin fara aiwatarwa bayan samun amincewar shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian.

Duk da cewa hukumomin Iran ba su fito fili sun bayyana cikakken abin da aka yanke ba, kamfanin dillancin labarai na Fars ya bayyana cewa kwamitin ya amince da shirin dawo da intanet ne da kuri’u tara na goyon baya. Rahoton ya ce yanzu ana jiran sahalewar shugaban ƙasa kafin a fara aiki da sabon tsarin.

Tun bayan ɓarkewar rikicin baya-bayan nan a ƙasar, yawancin ‘yan Iran sun shiga cikin matsalar rashin intanet, inda kaɗan daga cikin mutane masu amfani da “Internet Pro”, wasu katunan SIM na musamman da kuma tsarin Starlink ne kawai suka ci gaba da samun damar shiga yanar gizo.

Masana na ganin wannan katsewar ita ce mafi tsawo da Iran ta taɓa fuskanta a tarihin dakatar da intanet a ƙasar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *