Kwalejin Fasaha ta Moshood Abiola Polytechnic (MAPOLY) da ke Abeokuta ta kori ɗalibai 365 da ke karatun Babbar Diploma ta Ƙasa (HND).

Kwalejin Fasaha ta Moshood Abiola Polytechnic (MAPOLY) da ke Abeokuta ta kori ɗalibai 365 da ke karatun Babbar Diploma ta Ƙasa (HND).

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Yemi Ajibola, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa ɗaliban sun gabatar da sakamakon Diploma ta Ƙasa (ND) na ƙarya da kuma takardun bayanan karatu (transcripts) da aka ƙirƙira daga wasu cibiyoyi domin samun damar shiga makarantar.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan wani bincike mai zurfi da makarantar ta gudanar wajen tantance sahihancin takardun da aka gabatar yayin neman gurbin karatu da kuma lokacin rajista.

Makarantar ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau’in magudi ko rashin gaskiya a harkokin ilimi ba, tana mai cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da tsafta a tsarin karatunta.

Bayanan da makarantar ta fitar sun nuna cewa Makarantar Sadarwa da Fasahar Bayanai ce ta fi yawan ɗaliban da abin ya shafa, inda aka samu mutum 156. Sai Makarantar Kasuwanci da Nazarin Gudanarwa da ɗalibai 117, Makarantar Kimiyya da Fasaha mai 54, Makarantar Injiniya mai 36, yayin da Makarantar Nazarin Muhalli ke da ɗalibai biyu.

Shugaban makarantar, Dakta Koye Jolaoso, ya yi kira ga masu neman gurbin karatu da su kauce wa amfani da takardun bogi, yana mai cewa MAPOLY za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare martabar ilimi da tabbatar da nagarta a harkokin koyarwa da koyo.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *