Kotu Ta Wanke Murtala Garo Daga Zargin Cin Hanci da Rashawa

Babbar Kotun Jihar Kano ta kori karar zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, tare da wasu mutum biyar, sakamakon rashin bin ka’idojin bincike da kuma hurumin tuhuma. Alkalin kotun, Sanusi Ado Ma’aji, ne ya yanke hukuncin a zaman da kotun ta yi a Kano.

Kotun ta bayyana cewa ba zai yiwu a gurfanar da wanda ake zargi ba tare da gudanar da sahihin bincike ba, inda ta jingina da dokar gudanar da shari’ar laifuka ta 2019. Haka kuma ta yanke cewa hukumar Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission ba ta da hurumin binciken laifukan cin hanci, lamarin da ya sa aka warware batun gaba daya a bangaren wadanda ake tuhuma.

Tun da farko dai an zargi Garo da wasu da karkatar da sama da naira biliyan 57 na kudaden kananan hukumomi, tare da tuhume-tuhume da suka hada da hada baki da sata da karya doka.

Sai dai bayan wannan hukunci, kotun ta sallami dukkan wadanda ake kara, yayin da rahotanni ke cewa ana duba yiwuwar nada Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *