Jam’iyyar NDC ta ɗauki wani muhimmin mataki na siyasa a Jihar Kano bayan da ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zaɓi Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna domin zaɓen shekarar 2027.
Mustapha, wanda ɗa ne ga fitaccen ɗan siyasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taɓa zama Kwamishinan Matasa da Wasanni a gwamnatin Kano. Sai dai daga baya ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin gwamnatin jihar da tafiyar siyasar mahaifinsa.
Tabbatar da wannan zaɓi ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed, cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa Aminu Abdussalam Gwarzo ya amince da Mustapha Kwankwaso a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a karkashin jam’iyyar NDC a babban zaɓen shekarar 2027.
Masana harkokin siyasa na kallon wannan mataki a matsayin yunƙurin jam’iyyar NDC na ƙara samun karɓuwa da kuma ƙarfafa matsayinta a Kano, jihar da ke daga cikin wuraren da siyasa ke da tasiri sosai a Najeriya.

