Jam’iyyar APC za ta aiwatar da  zaɓen fid-da-gwani idan sulhu ya ci tura a  jIHAR Yobe — Mai Mala Buni.

Jam’iyyar APC za ta aiwatar da zaɓen fid-da-gwani idan sulhu ya ci tura a jIHAR Yobe — Mai Mala Buni.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa Jam’iyyar APC a jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da zaɓen fid-da-gwani idan har ƙoƙarin cimma matsaya tsakanin masu neman takara bai yi nasara ba kafin babban zaɓen 2027.

Buni ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan amincewa da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Baba Mallam Wali, a matsayin wanda jam’iyyar ta fi karkata a kai domin takarar gwamna.

A cewarsa, an cimma matsayar ne bayan wata ganawa ta masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar 23 ga Afrilu, 2026, inda aka nuna goyon baya ga Wali a matsayin ɗan takarar maslaha.

Sai dai gwamnan ya jaddada cewa idan har ba a samu cikakkiyar fahimta tsakanin dukkan ɓangarori ba, jam’iyyar za ta bi tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar gudanar da zaɓen fid-da-gwani cikin gaskiya da adalci.

“Mun taɓa irin wannan yanayi a baya. A shekarar 2019 an tsayar da ni ta hanyar maslaha, amma saboda wasu sun ƙi amincewa sai aka gudanar da zaɓe, kuma na samu nasara. Don haka idan buƙatar hakan ta taso a yanzu, a shirye muke,” in ji Buni.

Ya ce shugabannin APC na ci gaba da tattaunawa da masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an samu mafita cikin lumana da haɗin kai.

Gwamnan ya bayyana haɗin kai a matsayin ginshiƙin nasarar APC, yana mai cewa zaman lafiya tsakanin mambobin jam’iyyar zai taimaka wajen ƙarfafa damar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Buni ya kuma bayyana cewa duk masu neman muƙaman siyasa a jihar suna da niyyar yi wa al’umma hidima, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar za ta tafiyar da kowa ba tare da nuna bambanci ba.
A ƙarshe, ya yi kira ga ’ya’yan APC a Yobe su ci gaba da haɗa kai tare da ƙara bai wa jam’iyyar goyon baya yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *