Shugaban hukumar, Dakta Shamsuddeen Yahaya, ya ce har yanzu ba a tabbatar da bullar cutar ba kai tsaye, domin ana jiran sakamakon gwaje-gwajen da aka gudanar kan mutanen da ake zargi sun kamu.
Ya bayyana cewa jami’an lafiya na bai wa duk wanda ya nuna alamomin cutar kulawa ta musamman cikin gaggawa, musamman masu fama da matsanancin ciwon kai, amai da kuma maƙalewar wuya — waɗanda ake dangantawa da cutar sanƙarau.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tsananin zafi a Katsina da wasu sassan Najeriya, lamarin da masana ke cewa na iya taimakawa wajen yaɗuwar wasu cututtuka masu haɗari.
Dakta Shamsuddeen ya ce hukumomin lafiya sun tura jami’ai zuwa yankunan da abin ya shafa domin ɗaukar matakan kariya da hana yiwuwar ɓarkewar annoba.
Haka kuma ya ce ana haɗa kai da ƙungiyoyi da abokan hulɗa a fannin lafiya wajen wayar da kan jama’a, tattara bayanai da kuma tabbatar da an kai ɗauki cikin lokaci idan bukatar hakan ta taso.
