Gwamnatin Kebbi ta sanar da shirin aurar da zawarawa 300 a karo na uku a wani yunƙuri na tallafa wa mata marasa galihu da kuma kare tarbiyya da walwalar yara a jihar.

Gwamnatin Kebbi ta sanar da shirin aurar da zawarawa 300 a karo na uku a wani yunƙuri na tallafa wa mata marasa galihu da kuma kare tarbiyya da walwalar yara a jihar.

Kwamishinar Mata da Ci-gaban Yara, Hajiya Halima Hassan Kamba, ce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi kan ayyukan da ma’aikatar ta gudanar.

Ta ce a watan Yulin wannan shekara ne za a gudanar da shirin auren gata wanda zai haɗa ma’aurata 300 domin taimaka wa waɗanda matsin tattalin arziki ya hana su kafa iyali duk da suna da sana’o’i ko hanyoyin neman abinci.

A cewar gwamnatin jihar, manufar wannan shiri ita ce rage matsalolin zamantakewa da kuma tallafa wa mata marasa ƙarfi domin su samu ingantacciyar rayuwa.

Kwamishinar ta kuma bayyana cewa ma’aikatar na ci gaba da ƙoƙarin kare haƙƙin mata da yara tare da tabbatar da walwalarsu ba tare da nuna bambanci tsakanin mata da maza ba.

Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta gyara gidan kula da yara da ke Kawara tare da samar da kayayyakin da suka dace ga yaran, sannan an sake gyara gidan gyaran hali na yara domin inganta kulawa da su.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin cewa maimakon mayar da hankali kan aurar da zawarawa, ya kamata a fi ƙarfafa samar da ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai ga mata da matasa domin rage matsin rayuwa da talauci a Arewa.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *