Jami’an ’yan sanda sun cafke wani fasto mai suna Roman Samson, mai shekaru 45, bisa zargin haddasa mutuwar wata yarinya mai shekaru 13 mai suna Nancy Peter bayan ya yi mata bulala saboda zargin sata.
Lamarin ya faru ne a yankin Obanleku da ke Karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Riba, inda ya janyo ce-ce-ku-ce da damuwa a tsakanin mazauna yankin.
Mahaifiyar marigayiyar, Agnes Peter, ta bayyana cewa ta kai ’yarta wajen faston ne domin ya yi mata nasiha bayan wasu kuɗaɗe har Naira 30,000 da ta ajiye a gida sun ɓace. A cewarta, yarinyar ta amsa cewa ita ce ta ɗauki kuɗin tare da nuna inda ta ɓoye su.
Agnes ta ce bayan ta bar gidan faston domin bincika bayanan da ’yarta ta bayar, ta gano kuɗin kamar yadda aka bayyana. Sai dai da ta dawo, ta tarar faston na gaggawar kai yarinyar asibiti.
“Na same su a hanya suna kan hanyar zuwa asibiti. Ban san cewa an yi mata duka ba,” in ji mahaifiyar.
Bayan isa asibitin, likitoci sun tabbatar da rasuwar yarinyar.
Rahotanni sun nuna cewa faston ya amsa yi wa Nancy bulala bayan an sanar da shi cewa tana da halin sata, amma ya musanta zargin cewa ya yi hakan da nufin kashe ta. Ya ce ya yi matuƙar firgita ne lokacin da ya lura lafiyarta ta fara tabarbarewa, lamarin da ya sa ya garzaya da ita zuwa asibiti domin ceto rayuwarta.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba ta tabbatar da kama faston, tana mai cewa an fara gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Mutuwar yarinyar ta sake tayar da muhawara kan illar hukunta yara da duka da kuma hanyoyin da ya kamata a bi wajen gyara tarbiyyar yara ba tare da amfani da tashin hankali ba.
Mazauna yankin sun bayyana Nancy a matsayin yarinya mai fara’a da son jama’a, suna mai cewa rasuwarta ta bar babban gibi tare da jefa al’umma cikin alhini.
A yanzu haka, wanda ake zargin na tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike kafin ɗaukar matakin shari’a a kansa.

