Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga ’yan Najeriya da shugabanni su yi taka-tsantsan kan abubuwan da ka iya haddasa rikici, yana mai gargadin cewa wasu daga cikin matsalolin da suka kai ga yaƙin basasar Najeriya na shekarar 1967 har yanzu suna ci gaba da bayyana a cikin al’umma.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abeokuta yayin da ya karɓi tarin littattafai, bayanan bincike da kuma shaidun waɗanda suka tsira daga kisan gillar da aka yi a Asaba a lokacin yaƙin basasa.
Ya ce yaƙin da Najeriya ta yi na tsawon shekaru uku ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa, yana mai jaddada cewa bai kamata ƙasar ta sake fuskantar irin wannan mummunan yanayi ba.
A cewarsa, abin da ya faru a lokacin ya kamata ya zama darasi ga al’ummomin ƙasar domin kauce wa duk wani abu da zai iya kawo rarrabuwar kawuna ko tashin hankali.
“Mun taɓa shiga yaƙin basasa kuma mun ga irin illolin da ya haifar. Wannan kaɗai ya isa ya sa mu tabbatar da cewa ba za a sake komawa irin wannan yanayi ba,” in ji tsohon shugaban ƙasar.
Obasanjo ya kuma yabawa masu bincike da marubutan da suka tattara bayanai kan kisan gillar Asaba, yana mai cewa adana tarihi da rubuta abubuwan da suka faru na taimakawa wajen fahimtar gaskiya, samar da sulhu da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Ya bayyana cewa duk da kasancewarsa soja a lokacin yaƙin, ba shi ne ke jagorantar ayyukan sojoji a yankin Asaba ba. Sai dai ya ce daga baya an ba shi nauyin tabbatar da cewa an kare fararen hula daga duk wani nau’in cin zarafi bayan ƙarshen yaƙin.
Tsohon shugaban ƙasar ya sake nanata aniyarsa ta ci gaba da kira ga zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa makomar Najeriya na cikin haɗin kan al’ummarta da kuma koyon darasi daga kura-kuran baya.

