Ambaliyar a Jihar Legas ta jefa mazauna yankin Oshodi cikin tashin hankali bayan rushewar katangar sansanin sojojin sama.

Ambaliyar a Jihar Legas ta jefa mazauna yankin Oshodi cikin tashin hankali bayan rushewar katangar sansanin sojojin sama.

 

Mazauna titin Ayinke da ke unguwar Shogunle a yankin Oshodi na Jihar Legas na ci gaba da kirga asarar da suka yi bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a ranar Lahadi.

Ambaliyar ta lalata gidaje, motoci da kayayyakin amfani na yau da kullum, tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da rayuwar al’ummar yankin.

Mazauna yankin sun danganta tsanantar lamarin da rushewar wani ɓangare na katangar sansanin Sojojin Sama na Najeriya, wanda suka ce ya toshe hanyar magudanar ruwa, lamarin da ya sa ruwa ya mamaye gidaje, shaguna da manyan hanyoyi.

A yayin da jama’a ke kokarin farfaɗowa daga bala’in, an ga mutane da dama suna fitar da kayayyakinsu zuwa waje domin busar da su. Katifu, kujeru, tufafi, talabijin da sauran kayan gida na daga cikin abubuwan da ambaliyar ta shafa, yayin da wasu motocin da suka lalace aka garzaya da su wuraren gyara.

Wani mazaunin yankin mai suna Moses ya bayyana cewa aikin tsaftar muhalli da aka gudanar a kusa da sansanin sojojin saman ya haifar da toshewar hanyoyin ruwa, wanda daga bisani ya haddasa taruwar ruwa mai yawa da ya karya katangar sansanin.

A cewarsa, da zarar ruwan ya rasa hanyar wucewa, sai ya karkata zuwa gidajen jama’a inda ya haddasa babbar barna.

Ita ma wata ‘yar kasuwa, Bukola Fagbenro, ta ce ta yi asarar kayayyakin kasuwanci masu yawa sakamakon ambaliyar, tana mai cewa ba ta taɓa fuskantar irin wannan iftila’i ba tun bayan zamanta a yankin.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa saurin shigowar ruwan ya hana su ceto mafi yawan dukiyoyinsu, yayin da wasu iyalai suka shafe sa’o’i suna kwashe ruwa daga cikin gidajensu domin rage barnar da aka yi.

Bayan afkuwar lamarin, mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta kawo musu agajin gaggawa domin tallafa wa waɗanda suka yi asara, tare da ɗaukar matakan gyara magudanan ruwa da inganta tsarin tsaftar muhalli domin kauce wa sake faruwar irin wannan ambaliya a nan gaba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *