Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen shiyyar Kano, ta nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke jan ƙafa wajen aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 da aka cimma da ƙungiyar, tana mai gargadin cewa hakan na iya janyo sabon yajin aiki a jami’o’in da abin ya shafa.
Ko-odinetan ASUU na shiyyar Kano, Abdulrazaq Ibrahim, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya ce har yanzu jami’o’in jihohin Kano, Kaduna da Jigawa ba su fara aiwatar da muhimman sassan yarjejeniyar ba.
Ya ce duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wasu matakai na cika alƙawurran da ke cikin yarjejeniyar, musamman wajen sakin kuɗaɗen wasu alawus-alawus na malaman jami’o’in tarayya, gwamnatocin jihohin uku ba su nuna irin wannan ƙoƙari ba.
A cewarsa, jihohin sun kasance cikin tattaunawar da ta haifar da yarjejeniyar, amma har yanzu ba a ga sahihin matakin da zai tabbatar da aiwatar da abin da aka amince da shi ba.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatocin Kano, Kaduna da Jigawa da su gaggauta warware matsalolin da ke tsakanin su da malaman jami’o’i, tare da biyan dukkan haƙƙoƙin da ake binsu domin kauce wa tangarɗar da za ta iya shafar harkokin karatu.
ASUU ta kuma sake jaddada buƙatarta na a biya mambobinta albashin watanni uku da rabi da aka riƙe musu, tare da tabbatar da tura kuɗaɗen fansho da sauran haƙƙoƙin ma’aikata ba tare da ƙarin jinkiri ba.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ci gaba da yin biris da waɗannan buƙatu na iya tilasta mata ɗaukar matakan da suka haɗa da dakatar da ayyukan koyarwa.

