Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe makarantar marayu ta Daarul Kitab Islamiyya da ke Zariagi a Ƙaramar Hukumar Adavi, bayan harin da ’yan bindiga suka kai makarantar tare da yin garkuwa da yara 26 da wasu mutane.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai farmaki makarantar ne a ranar 26 ga Afrilu, 2026 inda suka sace ɗalibai tare da matar wanda ya mallaki makarantar.
Bayan harin, jami’an tsaro sun samu nasarar ceto mutum 17 cikin waɗanda aka sace, yayin da dakarun soji suka kuɓutar da sauran mutum tara a ranar 7 ga watan Mayu kafin daga bisani aka haɗa su da iyalansu.
A sakamakon lamarin, Kwamishinan Ilimi na jihar, Wemi Jones, ya jagoranci tawagar jami’an ma’aikatar ilimi zuwa makarantar inda aka bayar da umarnin rufe ta nan take.
Gwamnatin ta bayyana cewa makarantar ta fara aiki ne ba tare da samun cikakkiyar amincewa daga hukumomin jihar ba, lamarin da ya sa aka dakatar da dukkan harkokin karatu a wurin.
Kwamishinan ya ce makarantar ba za ta sake buɗewa ba har sai gwamnati ta tabbatar da cewa an cika duk sharuddan da suka dace na gudanar da makaranta mai inganci da tsaro.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da sa ido kan makarantu domin tabbatar da tsaron ɗalibai da ingancin ilimi a faɗin jihar baki ɗaya.

