Gwaman Uba Sani ya ce ayyukan Tinubu a Jihar Kaduna sun cancanci a sake kada masa da ƙuri’u a Zaben 2027.

Gwaman Uba Sani ya ce ayyukan Tinubu a Jihar Kaduna sun cancanci a sake kada masa da ƙuri’u a Zaben 2027.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa ayyukan ci gaba da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a jihar sun cancanci al’ummar Kaduna su nuna godiya ta hanyar ba shi gagarumin goyon baya a babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin ƙaddamar da wasu sabbin ayyukan tituna guda 11 a ƙananan hukumomin Zariya da Sabon Gari. Ya ce gwamnatin tarayya ta zuba jari sosai wajen bunƙasa ababen more rayuwa a jihar, ciki har da amincewa da aikin jirgin ƙasa na cikin birni (Light Rail) mai darajar tiriliyan Naira 1, wanda ya ce za a fara aiwatar da shi cikin watanni biyu masu zuwa.

Uba Sani ya kuma sanar da cewa aikin titin Mando zuwa Birnin Gwari zai fara cikin mako guda, bayan shugaban ƙasa ya amince da sakin sama da Naira biliyan 100 domin gudanar da aikin.

A cewarsa, gwamnatinsa ta ƙaddamar da ayyukan tituna 150 masu tsawon sama da kilomita 1,355 a faɗin jihar, inda aka riga aka kammala yawancinsu, yayin da ake sa ran kammala sabbin ayyukan da aka ƙaddamar cikin watanni biyar.

Shi ma Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yaba da irin tallafin da gwamnatin Tinubu ke bai wa jihar Kaduna, musamman a fannonin ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce waɗannan matakai za su ƙara yawan jami’o’in gwamnatin tarayya da ke jihar zuwa guda biyar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *