Cire Tallafin Fetur  Shine ‘yan Hana Najeriya Faɗawa Matsalar Tattalin Arziki — Cewar Tinubu

Cire Tallafin Fetur Shine ‘yan Hana Najeriya Faɗawa Matsalar Tattalin Arziki — Cewar Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matakin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta aiwatar ya taimaka wajen ceto Najeriya daga shiga wani mawuyacin hali na tattalin arziki.

Tinubu ya yi wannan bayani ne a Legas lokacin da wasu gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasar suka kai masa ziyarar barka da Sallah tare da taya gwamnatinsa murnar cika shekaru uku a kan mulki.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci ziyarar akwai na Legas, Nasarawa, Jigawa, Sakkwato, Kebbi, Taraba, Neja, Ekiti, Delta, Ondo, Edo, Adamawa, Benue, Enugu, Ogun da Kogi. Haka kuma, mataimakan gwamnonin Borno da Kano sun kasance cikin tawagar.

Shugaban ƙasar ya amince cewa cire tallafin fetur ya jefa al’ummar Najeriya cikin ƙalubale da tsadar rayuwa, amma ya jaddada cewa matakin ya zama dole domin kare tattalin arzikin ƙasar da kuma tabbatar da dorewar harkokin kuɗaɗen gwamnati.

A cewarsa, duk da wahalhalun da ake fuskanta sakamakon sauyin, gwamnatin tarayya na ci gaba da ɗaukar matakan rage tasirin da matakin ya yi wa rayuwar jama’a tare da inganta tattalin arzikin ƙasar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *