Shugabu Tinubu ya yi alƙawarin amfani da fasaha da bayanan sirri wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.

Shugabu Tinubu ya yi alƙawarin amfani da fasaha da bayanan sirri wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da sabbin fasahohi da ingantattun dabarun tattara bayanan sirri domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro da ke addabar sassan Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a wajen bikin Ranar Sojin Najeriya ta shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta dukufa wajen samar wa rundunar sojoji kayan aiki na zamani da kuma horas da jami’ai domin su dace da sabbin ƙalubalen tsaro da ke tasowa a duniya.

Shugaban ƙasar ya ce daga cikin matakan da ake ɗauka akwai ƙarfafa masana’antun tsaro na cikin gida, musamman Kamfanin Masana’antun Tsaro na Najeriya (DICON), domin bunƙasa ƙera kayan aikin soja a gida da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da dukkan kayan aikin da suka dace domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.

Tinubu ya kuma yabawa dakarun sojin Najeriya bisa rawar da suke takawa wajen kare haɗin kan ƙasa da kuma fuskantar barazanar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffukan da ke barazana ga zaman lafiya.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara mayar da hankali wajen inganta walwala da jin daɗin jami’an soji domin ƙarfafa musu guiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare martabar Najeriya da kuma tsaron al’umma duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Jawaban sun fito ne yayin da gwamnati ke ci gaba da neman sababbin hanyoyi da dabaru domin magance matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar wasu sassan ƙasar.

 

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *