Peter Obi ya bayyana muhimman tsare-tsarensa da cigaban da zai kawo idan ya lashe zaɓen 2027.

Peter Obi ya bayyana muhimman tsare-tsarensa da cigaban da zai kawo idan ya lashe zaɓen 2027.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana wasu daga cikin manyan manufofin da gwamnatinsa za ta aiwatar idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Obi ya ce babban burinsa shi ne gina Najeriya mai cike da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba, inda kowane ɗan ƙasa zai samu damar cin gajiyar albarkatun ƙasar.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar jama’a, yaƙi da almundahana da kuma samar da ingantaccen tsarin shugabanci da zai tabbatar da adalci, wadata da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

Obi ya jaddada cewa ilimi da kiwon lafiya su ne tubalan gina kowace al’umma mai ci gaba, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta kai ga ci gaba mai ɗorewa idan ba ta ba da muhimmanci ga bunƙasa albarkatun ɗan Adam ba.

A cewarsa, ɗaya daga cikin matakan farko da gwamnatinsa za ta ɗauka shi ne kafa wani kwamiti na musamman da zai jagoranci yaƙi da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da samar da hanyoyin da za su tabbatar da samun ilimi mai inganci ga yara a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa ilimin sana’o’i da koyon fasaha domin bai wa matasa damar samun ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun aikin yi ko kuma kafa sana’o’insu.

Obi ya bayyana cewa za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin addini wajen samar da cibiyoyin horas da sana’o’i da kayan aiki na zamani, tare da amfani da wasu tsare-tsaren koyon aiki da suka yi nasara a ƙasashe masu ci gaba.

Ya ce ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu ita ce rashin daidaito tsakanin ilimin da ake koyarwa da buƙatun kasuwar aiki, lamarin da ke haddasa yawaitar rashin aikin yi duk da buƙatar ƙwararrun ma’aikata a fannoni da dama.

A ƙarshe, Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki wajen daidaita tsarin ilimi da bukatun tattalin arziki domin samar da matasa masu ƙwarewa, waɗanda za su iya dogaro da kansu tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *