Sama da ’Yan Najeriya Miliyan 1.5 Sun Yi Sabuwar Rajistar Katin Zaɓe — INEC

Sama da ’Yan Najeriya Miliyan 1.5 Sun Yi Sabuwar Rajistar Katin Zaɓe — INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa mutane 1,565,873 ne suka yi rajistar katin zaɓe a cikin makonni bakwai da suka gabata, zuwa ranar 26 ga watan Yuni.

Bayanan da hukumar ta fitar a Abuja sun nuna cewa daga cikin adadin, mutum 620,933 sun fara rajistar tasu ta yanar gizo, yayin da mutum 944,940 suka kammala dukkan matakan rajista a cibiyoyin da hukumar ta tanada a faɗin ƙasar nan.

Sai dai INEC ta bayyana cewa waɗannan alkaluma na wucin gadi ne, domin har yanzu ana ci gaba da tantance bayanan masu rajista domin gano maimaituwa ko wasu kura-kurai kafin fitar da adadi na ƙarshe.

Rahoton ya nuna cewa Jihar Kano ce ke kan gaba wajen yawan sabbin masu rajista da mutum 118,207, sai Jihar Legas da mutum 78,360, yayin da Jihar Delta ke biye da mutum 76,395.

Hukumar ta kuma sanar da dakatar da aikin rajistar katin zaɓe na ɗan lokaci a jihohin Ekiti da Osun saboda shirye-shiryen zaɓukan gwamna da ake gudanarwa a jihohin, kamar yadda Dokar Zaɓe ta shekarar 2022 ta tanada.

A fannin sana’o’i, ɗalibai ne suka fi rinjaye a cikin sabbin masu rajistar da mutum 384,093. Haka kuma, ’yan kasuwa sun kai mutum 333,539, yayin da manoma da masu kamun kifi suka kai mutum 273,627.

Bugu da ƙari, INEC ta ce mutane 18,919 masu buƙata ta musamman sun samu nasarar yin rajistar katin zaɓe a wannan lokaci.

Hukumar ta yi kira ga dukkan ’yan Najeriya da suka kai shekarun kaɗa ƙuri’a amma har yanzu ba su yi rajista ba da su yi amfani da damar da ake da ita ta hanyar shiga shafin hukumar ko ziyartar cibiyoyin rajista mafi kusa da su domin samun damar shiga zaɓukan da za a gudanar nan gaba.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *