Hukumar NDLEA ta Lalata Muggan Kwayoyi sama da Kilo 12,000 a Jihar Kano.

Hukumar NDLEA ta Lalata Muggan Kwayoyi sama da Kilo 12,000 a Jihar Kano.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Kano ta sanar da lalata miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 12,233.946 da aka kama a lokuta daban-daban a fadin jihar.

Mai magana da yawun hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce matakin wani bangare ne na ci gaba da yaki da fatauci da amfani da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya ce nasarar ta samu ne karkashin jagorancin Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal, wanda ke jagorantar ayyukan da suka shafi bincike, kama masu laifi da kuma dakile safarar miyagun kwayoyi.

A cewar sanarwar, lalata kwayoyin da aka kama na nuna kudurin hukumar na ci gaba da gano masu aikata irin wadannan laifuka, kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Daga cikin miyagun kwayoyin da aka lalata akwai tramadol, tabar wiwi, hodar iblis, pregabalin da wasu nau’ikan kayan maye da aka kwato daga wurare daban-daban a Kano.

Hukumar ta bayyana cewa an samu wasu daga cikin kwayoyin ne ta hanyar samame da binciken da aka gudanar a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da kuma wasu sassan birnin Kano da kewaye.

NDLEA ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da yaki da safara da dillancin miyagun kwayoyi a fadin jihar, tana mai cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an rage ko an kawar da matsalar shaye-shaye da fataucin kayan maye a Kano.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *