Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe Naira miliyan 273.29 domin gina gidajen noma na zamani guda 20 a ƙananan hukumomi 10 na jihar, da nufin bunƙasa harkar noma da samar wa matasa ayyukan yi.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta.
Ya ce aikin ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar na ƙarfafa noman zamani da kuma amfani da damar da Jigawa ke da ita a fannin noma.
Musa ya ƙara da cewa gidajen noman za su kasance a ƙananan hukumomi 10 da aka zaɓa, tare da bai wa matasa 82 da aka horas damar amfani da ƙwarewar da suka samu wajen gudanar da ayyukan noma na zamani.

