Babban sufeton yan Snada na Kasa IGP Disu ya Jaddada Ƙudirin Yaƙi da ‘Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Fadin Najeriya.

Babban sufeton yan Snada na Kasa IGP Disu ya Jaddada Ƙudirin Yaƙi da ‘Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane a Fadin Najeriya.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasar nan.

Disu ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Zamfara a ranar Talata, inda ya jagoranci jami’an tsaro, iyalan mamatan da sauran al’umma wajen gudanar da sallar jana’izar jami’an ‘yan sanda uku da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikinsu.

Yayin da yake jawabi a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da ke Gusau, Sufeto Janar ɗin ya bayyana jami’an da suka rasu a matsayin gwarazan da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da yaƙi da ta’addanci.

Ya ce sadaukarwar da suka yi ba za ta tafi a banza ba, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da matsa kaimi wajen yaƙi da miyagun laifuka da tabbatar da zaman lafiya a ƙasa.

Ziyarar ta kuma kasance wata dama ta nuna alhini da jajantawa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara kan rashin jami’an, tare da ƙarfafa gwiwar jami’an da ke ci gaba da fafatawa da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.

Manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ne suka halarci tarbar IGP ɗin, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Nakwada, wanda ya wakilci Gwamna Dauda Lawal a wajen jana’izar.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *